Fasa rumbunan abinci ya saba da addini
October 28, 2020Ci gaba da fuskantar wannan matsala ta farfasa rumbunan adana kayayyaki na gwamnati da ma na al'umma'ar da ba su ji ba su gani ba da matasa zauna gari banzan suka dauka a matsayin sabon salon a kwata da karfin tuwo, ya daga hankalin gamayyar kungiyoyin Kristocin arewacin Najeriya. Kungiyar ta ce hakan ya yi kama da komawa zamani na jahiliyya ko zama da dabbobi a dokar daji ke yi, inda mai karfi ke bugewa ya dauka, abin da ke da hatsari ga makomar kasar domin nuna tamkara babu doka da oda ne.
Karin Bayani: Sauraron korafin kisa a zanga-zangar Lagos
Yadda matasan suka yi wa masu zanga-zangar neman sauyi a aikin 'yan sanda kutse, inda suke ci gaba da fasa wurare musamman a Abuja. Koda a ranar Talatar da ta gabata ma, sai da matasan da ake ganin sun yi wa masu Zanga-zangarkutse, suka yi diran mikiya a kan wurare da dama da suka hadar da sansanin masu yi wa kasa hidima da wurin da ake ajiye Babura, suka yi tayin awon gaba da su kafin sojoji su katse hanzarinsu.
Kurari da ma tsawa da sifeto janar na 'yan sanda 'yan sandan Najeriya da ma babban hafsan sojin kasar suka yi, na dauka mataki domin kare kasar daga wannan abin kunya na wasoso da ma sata da tsakar rana da sunan dibar ganima ta kayan tallafi cutar COVID-19, ya sanya tsohon shugaban Najeriyar Abdulsalami Abubakar kai wa ga sanya baki a cikin lamarin a kokari na tsawataya da ma lallashi yana mai cewa.
Karin Bayani: Najeriyar na fama da jerin zanga-zanga
A yayin da jami'an tsaron ke kara jajircewa domin maido da doka da oda, gamayyar kungiyar Kiristocin Najeriyar ta bukaci shugabanin manyan addinai biyu na Musulmi da Kirista da su kara ba da agajinsu, a kokari na maido da doka da oda da ma yakar duk wasu shaidanu da ke cikin lamarin, tare da neman daukar mataki a kan jami'an gwamnati da aka ba su amana ta rarraba kayayyakin tallafin da suka ajiye ba tare da wani dalili na zahiri ba.