1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Fargabar barkewar rikici

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 22, 2020

Yayin da zanga-zangar da matasa ke yi a Tarayyar Najeriya ke rikedewa zuwa tashin hankali a wasu sassan kasar, ana fargabar barkewar rikicin addini da kabilanci.

https://p.dw.com/p/3kIrZ
Nigeria Ikeja | End Sars Proteste | Demonstranten
Hoto: Pius Utomi EkpeiAFP/Getty Images

Zanga-zangar dai ta faro ne makonni biyun da suka gabata, a matsayin ta lumana da nufin kawo karshen rundunar 'yan sandan musamman masu yaki da fashi da makami wato SARS. Sai dai ko bayan rushe rundunar ta SARS da maye gurbinta da rundunar SWAT sakamakon matsin lambar matasan masu zanga-zanga, ba ta sauya zani ba domin kuwa sun ci gaba da yin kira da a gudanar da sauye-sauye a rundunar 'yan sandan da ma bangaren tsaro baki daya.

Zanga-zangar ta fantsama a sauran sassan kasar, inda a arewacin kasar suke yin kira da a kawo karshen rashin tsaro. Sannu a hankali kuma, zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali a wasu sassan kasar, ciki kuwa har da jihohin Lagos da Kano da kuma Plateau.

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna

Rahotanni da Sharhuna