1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Watsi da nadin kwamishiniyar INEC

Uwais Abubakar Idris LMJ
July 13, 2021

Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da Lauratta Onochie wacce shugaban kasar Muhammadu Buhari ya aika sunanta, yana neman a amince da ita a matsayin kwamishinyar hukumar zabe.

https://p.dw.com/p/3wQvs
Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Wannan mataki da majalisar dattawan Najeriyar ta dauka  dai, ya yi wa 'yan adawa da kungiyoyin kare hakkin dan Adam dadi. Ana dai kallon matakin a matsayin wankan tsarki da zai kare martabar majalisar dattawan ta yi wa kanta, bayan ta ki amincewa da nadin Laurreta Onochie a matsayin kwamishiniyar hukumar zaben ta kasa INEC. A yanzu dai kanwa ta kar tsami kan wannan batu da ya haifar da cece-kuce har ma da zanga-zanga a Najeriyar, musamman daga babbar ta PDP da kungiyoyin kare hakkin dan Adam.

Karin Bayani: Mafita kan makomar zaben 2023 a Najeriya

Mr Deji Adeyanju na kungiyar Concern Nigeria, ya bayyana cewa matakin da majalisar ta dauka ya nuna samun nasarar matsin lambar da suka yi. Ba kasafai dai majalisar dattawan ke kin amincewa da bukatar da shugaban kasar ya gabatar mata ba. Majalisar dattawan ta kuma amince da kafa hukumar kula da kararrakin zabe a Najeriyar, a kokarin tsaftace harkar. Ana dai kallon da ma yi wa wannan lamarin fassarar cewa akwai bukata a tsakanin 'yan adawa da na jam'iyyar APC mai mulki na bani gishiri in baka manda, domin wasu bukatu da za a nemi 'yan adawar su marawa 'ya'yan jam'iyya mai mulkin baya a nan gaba.