1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: Zabukan fid da gwani

Ma'awiyya Abubakar Sadiq Fati Muhammed(Ibrahima Yakubu) Mohamed Bello
May 27, 2022

A Najeriya yayin da jam’iyyun siyasa suka gudanar da zaben fid da gwani, a wasu jihohin zaben ya bar baya da kura musamman a jam'iyyun PDP da APC mai mulki.

https://p.dw.com/p/4Bxv4
Najeriya zaben shugaban kasa na 2015
Hoton jami'in zabe na dauke da akwatin zabeHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Aisha Binani ta kafa tarihi: Zaben fitar da gwani da aka gudanar a jihar Adamawa a jam'iyyar APC ya bude wa al'ummar jihar wani sabon babi a fagen siyasa, inda kallabi tsakanin rawuna ta fafata da 'yan takara biyar kuma ta dokesu. Sanata Aishatu Dahiru Binani ta kafa tarihi ne bayan da ta lashe zaben da kuri’u 430 a gaban abokan hamayyarta maza, ta kuma zama mace ta farko da ta kafa wannan tarihi, bayan da ta doke tsohon shugaban hukumar EFCC Malam Nuhu Ribadu da ya samu kuri'u 288, a yayin da tsohon gwamnan Adamawa Bindow Jibirila ya lashe kuri'a 103. Wannan wata alama ce da ke nuna cewa za a fafata a zaben gwamna da ke tafe tsakanin jam'iyyar APC da PDP ganin cewa Adamawar ce mazabar tsohon mataimakin shugaban kasa Abubakar Atiku kuma jigo a jam'iyyar ta PDP.

A Jihar Kano dan takarar jam'iyyar APC mai mulkin jihar Sha'aban Ibrahim Sharada ya yi watsi da sakamakon zaben fidda gwanin jihar inda ya kalubalanci zaben mataimakin gwamnan jihar Nasiru Gawuna a matsayin wanda zai tsaya takara a zaben gwamna da sunan APC. A jam'iyyar PDP mai adawa ana fuskantar cece-kuce bayan da aka fitar da cewa Muhammed Abacha ne dan takarar jam'iyyar a yayin da bangaren Sadik Wali ne dan takarar jam'iyyar daga bisani, wanda ke zama babban kalubale ga jam'iyyun duba da yadda jam'iyyar NNPP da bata jima da kafuwa ba a jihar ta fara girkuwa ta take samun karbuwa.

Karin Bayani: Najeriya siyasar jihar Kano na fama da rudani

A Jihar Sokoto zaben ya bar baya da kura

Nigeria zaben shugaban kasa malan zabe na shirya akwatan zabe
Malaman zabe na lura da akwatunan kada kuri'aHoto: Getty Images/AFP/L. Tato

Takaici ya mamaye wasu 'yan jam'iyyar PDP a jihar Sakkwato, jim kadan bayan da aka zabi Alhaji Sa’idu Umar sakamakon sasantawar da aka yi kafin a kada kuri’a amincewa da shi a matsayin dan takarar gwamnan jihar Sakkwato karkashin inuwar jam’iyyar ta PDP, inda tsohon kwamishinan muhalli Sagir Bafarawa dan tsohon gwamna Attahiru Bafarawa zai kasance a matsayin mataimaki.

Sai dai a fusace wasu magoya bayan jam'iyyar kamar Yusuf Abubakar a jam'iyyar ta PDP a jihar na cewa "Tun kafa tarihin siyasar jihar Sakkwato ba a taba ganin wanda ya ci amanar jam’iyyar tare da tozartar da al’umma jihar Sakkwato da cin zarafin matasan jihar Sakkwato kamar Aminu Waziri Tambuwal ba.

A jam'iyyar APC mai adawa a jihar Ahmad Aliyu tsohon mataimakin gwamnan Tambuwal a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC daga cikin 'yan takara shida da suka fafata a zaben fidda gwanin, sai dai dan Majalisar wakilai Hon. Abdullahi Balarabe Salame da ya fice daga zaben ya bayyana kura-kurai da bai gamsu da su ba.

A jihar Filato Zaben fid da gwani a jama'iyyar APC jihar ya bar baya da kura, bayan wasu daga cikin yan takara na jam'iyyar suka fice daga harabar zaben cikin fushi.

A Jiahr Kebbi ‘yan takara uku ne suka fafata a jam’iyyar APC mai mulkin jihar, sai dai Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu ya samu nasara, a yayin da a bangaren jam’iyyar PDP ‘yan taka biyar ne suka fafata kuma Manjo Janaral Aminu Bande ya samu nasara.

Haka batun yake a jihar Katsina, inda jam'iyyar APC ta zabi Dikko Umaru Radda a matsayin dan takarar gwamnan jihar, a yayin da ita kuwa jam'iyyar PDP mai adawa a jihar ta zabi Yakubu Lado Dan Marke a matsayin wanda zai kasance dan takarata a zaben jihar na gwamna mai tattare da kalubalen tsaro.

Karin Bayani: Najeriya amfani da kudi wajen fitar da 'yan takara

A Jihar Bauchi Tsohon shugaban rundunar najeriya ta sojan sama Sadique baba Abubakar ne ya lashe zaben fitar da gwani a jam'iyyar APC bayan da ya kada abokan hamayyarsa.

Yadda zaben ya wakana a yankin Kudu Maso Gabas

Nigeria hoton kada kuri'a a zaben Najeriya
Tana kada kuri'a a zaben NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/Sunday Alamba

Zaben fid da gwani a kujerar gwamna daga jamiyyun PDP da APC da sauran jamiyyu gudana a jihohi daban-daban na Kudu maso gabashin Najeriya kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta tsara. Sai dai an koka da yadda deleget-deleget su ka yi ta cin kasuwar su da tsinke, kuma 'yan takara sun yi ta kokawa da danniya da murda-murda da nuna karfin uban gida. 

A Jihar Rivers tsohon ministan sufir Rotimi Amaechi na ci gaba da dagewa wajen ganin M.Tonye Cole da yake goyon baya ya kai labari a jam'iyyar APC, lamarin da ke shan suka daga Sanata Magnus Abbey da shi ma ke neman darewa kan kujerar, ita kuwa jam'iyyar PDP Ama Opu Senibo Sim Fubara ne ya yi nasara ba tare da wata hamayya ba.

A Enugu magoya bayan jam'iyyar PDP sun tsayar da Peter Mbaa matsayin dan takarar gwamnan jihar. Shi kuwa Uche Nnaji kuma ya lashe zaben dan takarar na gwamna a jamiyyar APC, sai dai an samu banbanci a jam'iyyar a jihar Akwa Ibom, inda bangarori biyu suka gudanar da zaben kuma daga karshe suka ce za su nufi kotu.