1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 50 bayan yakin Biafra a Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 16, 2020

A ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1970 ne, aka kawo karshen yakin basasa a Najeriya wanda ya lakume rayukan mutane masu tarin yawa, mafi akasari yara kanana da tsofaffi.

https://p.dw.com/p/3WIff
Nigeria Eisenbahn Ogbete Markt
Hoto: DW/K. Gänsler

Laftanar Kanal Chukwuemaka Odumegwu Ojukwu  ne dai ya ayyana ballewar yankin Kudu maso Gabashin kasar, tare da ayyana 'yancin cin gashin kai a shekara ta 1967, biyo bayan wani juyin mulki da sojoji suka yi. Tun daga wannan lokacin, kasar ta tsunduma cikin halin yakin basasa da aka kwashe sama da shekaru biyu ana gwabzawa. Babban abin damuwar dai shi ne, har kawo yanzu al'ummomin da ke zaune a yankin na Kudu maso Gabashin Najeriyar, na ganin mahukunta ba sa yi musu adalci, inda har yanzu suke kokarin ballewa domin kafa kasar Biafra.