Matsalar tsaro na yawaita a Najeriya
September 30, 2020Shekaru 11 ke nan dai ake fama da hare-haren kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a kasar, ke taimakawa wajen dagula komai na ci-gaba a yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar.
Karin Bayani: Makomar 'yan matan Chibok
Tun lokacin da yankin ke dunkule a matsayin jiha guda kawo lokacin da aka raba shi zuwa jihohi shida dai, a iya cewa an samu ci gaba ta fannonin kusantuwar gwamnati da al'umma da kuma wadatuwar cibiyoyin lafiya da manya gami da kananan makarantu, da suka saukakewa al'ummar yankin damar yin karatu.
Karin Bayani: Kisan gillar ma'aikatan agaji a Najeriya.
To sai dai a sauran fannonin rayuwa a yankin ba su samu bunkasa yadda ya kamata ba, domin kuwa ba a iya amfani datarin arziki da ke kwance a cikinsa. A shekarun da su ka gabata, matsalar tsaro ta sake haifar da koma baya ga dan guntun ci-gaba da ka samu a yankin, musamman ma a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.
Ambasada Ahmed Umar Bolori jakadan zaman lafiya a Najeriya ne, a ganinsa duk ci-gaban da aka samu tun da ba zaman lafiya to ya zama na mai hakar rijiya. Ga masu fafutukar kare hakkin mata kamar A'ishatu Alhaji Kabu Damboa kuwa,
matan na daga cikin wadanda aka bari a baya in ana maganar ci-gaba ne a yankin na Arewa maso Gabashin Najeriyar.
Karin Bayani:
Dangane da tabarbarewa tsaro gwamnan jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni ya ce an samu sauki kuma mutane su kara hakuri za a kawo karshen sa. Yanzu haka dai ana sa ran cewa yunkurin da gwamnonin yankin na Arewa maso Gabas, suka iya na hukuma da za ta mayar da hankali wajen bunkasa shi, al'amura za su sauya matukar aka aiwatar da abubuwan da aka yi nufi cikin gaskiya.