Nijar ta kori jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya
October 11, 2023A wata wasika ce da hukumomin mulkin sojan kasar ta Nijar suka aika wa Babban Sakataren MDD suka sanar masa da wannan mataki na bai wa jakadiyar MDD a Nijar Mme Louise Aubin wa'adin kwanaki uku na ta tattare irin 'ya nata 'ya nata ta bar kasar. Hukumomin sojan kasar ta Nijar sun ce sun dauki wannan mataki ne a matsayin martani ga abin da suka kira zagon kasa da Babban Sakataren MDD a bisa tunzurin kasar Faransa yake yi wa Nijar ta hanyar haramta wa tawagar jami'anta shiga zauran tarukan kungiyoyin kasa da kasa da ma na MDD.
Amirka ta dakatar da tallafin da take bai wa Nijar
Wannan sabon takun saka da aka shiga tsakanin gwamnatin mulkin sojan Nijar da MDD ya zo ne a daidai loakcin da kasar Amirka ta sanar da daukar matakin katse tallafin kudi sama da miliyan 442 na Dalar Amirka ga fannin tattalin arzikin Nijar da kuma dakatar da tallafin da take baiwa kasar a fannin tsaro da kuma horas da sojojin kasar a fannin yaki da ta'addanci.
Nijar na ci gaba da katse hulda da kasashen duniya
Da yake tsokaci kan wannan batu Malam Alassan Intinakar shugaban jam'iyyar Akalkasa dan takara a zaben shugaban kasar da ya gabata ya ce abin da ya rage a yanzu shi ne korar sojojin Amirkar daga Nijar baki daya. Yanzu haka dai kasashen duniya na ci gaba da daukar matakin mayar da Nijar saniyar ware, inda ko a farkon wannan mako aka haramta wa tawagar Nijar shiga zauran taron Babban Bankin duniya da Asusun ba da Lamuni(IMF) da ke gudana a birnin Marrakech na kasar Maroko.