1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Jamus za su fice daga Nijar

Salissou Boukari AH
July 8, 2024

Hukumomin tsaro na kasar Jamus sun sanar da aniyarsu ta rufe sansanin sojin sama na kasar ta Jamus da ke a birnin Yamai.

https://p.dw.com/p/4i1NT
Hoto: Lisi Niesner/REUTERS

 A baya dai an samu wata kwarya-kwaryar yarjejniya tsakanin hukumomin na Nijar da kasar ta Jamus dangane da ci gaban kasancewar sojojin na Jamus a Nijar duk kuwa da cewa Nijar din ta umarci sojojin Faransa da ma na Amirka su fice daga kasar. Sai dai kuma bisa dukkan alamu ya zuwa yanzu ba samu wata cikakar jittuwa ba tsakanin bangarorin biyu wanda hakan ta sanya hukumomin tsaron na Jamus sanar da cewa Jamus din za ta dakatar da aiki a wannan sansani nata na sojojin sama nan zuwa karshen watan Augusta da   ke tafe.

Jamus ba ta amince da huldar Nijar da Rasha ba

Mali Bundewehr UN-Einsatz
Hoto: Alexander Koerner/Getty Images

Sai dai masana harkokin diflomasiyya irin su Hon. Moutari Ousmane tsohon Ambasada kuma tsohon dan majalisar dokoki na ganin cewa janyewar ba ta rasa nasaba da rashin ba su rigar kariya ta shari'a, amma kuma duk da haka a cewar sa dakatar da huldar soja bai zai hana wacan hulda ta diflomasiyya ba.Tuni dai masu sharhi ke ganin cewa Jamus da sauran kawayenta na kasashen yamma ba su yarda da yadda hukumomin na Nijar ke kara kusantar Rasha da  Iran ba.

Gwamnatin Nijr ba ta ce komai ba har yanzu a kan wannan furci

Symbolbild Drohne Bundeswehr
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa ko wani martani daga hukumomin Nijar kan wannan batu na dakatar da aikin rundunar sojojin saman na Jamus a Nijar.