Gwamnatin Njaeriya ta soki matakin Twitter
June 3, 2021Tun baya share wani sako da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sa a kafar ta Twitter dai rikici ya barke a tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin na sada zumunta. Mahukunta a Abuja ba su boye rawar kafar mai tasiri a kokari na tada hankula da hargitsa lamura cikin kasar da ke neman mafita a cikin rikicin rashin tsaron da ya rikide ya zuwa bakar siyasa a tsakanin sassan kasar.
Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed dai ya ce twitter na da manufar boye bisa rawar da take takawa cikin kasar a halin yanzu. Kuma kama daga daukar nauyin matasan ENDSARS da suka koma wasoso a shekarar da ta shude, ya zuwa zama kakakin masu neman da su balle Lai Muhammad ya ce Twitter ta yi nisa a kokarin hargitsa lamuran a kasar.
Karin Bayani: Umarnin da IPOB ta bayar ya karbu a Najeriya
Wannan ne dai karo na farkon fari da gwamnatin kasar ke fitowa fili domin nunin bacin rai bisa rawar kafafe na zumuntan da sannu a hankali ke komawa filin dagar rikici na siyasa a kasar. To sai dai kuma korafin na zaman alamun hanyar hada wando wuri guda da twitter da ya zuwa yanzu ke zaman ta kan gaba a tsakanin sadarwar 'yan boko na kasar.
Nigeria dai na zaman kasa ta kan gaba ga masu amfani da kafar ta twitter a nahiyar Africa, kuma duk wani mataki na iya kai wa ga jawo matsala ga kasuwa ta kamfanin da ke dada girma a nahiyar.
Barrister Saidu Tudun Wada dai na zaman wani lauya mai zaman kansa a tarrayar Najeriya, da kuma ya ce ba hujjar kyale kamfanin cin karensa har gashi a cikin sunan 'yanci na 'yan kasa. Kuma Kama daga India ya zuwa Australiya da Iran dama ragowa na kasashen duniya da daman gaske dai sun shiga rika takun saka da kamfunan sadarwar a kokarin daidaito a tsakanin 'yancin a fadar da makomar al'umma na kasashen daban-daban.