1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Umarnin IPOB na zaman dirshan ya samu karbuwa

Muhammad Bello AMA
May 31, 2021

A Najeriya mazauna jihohi biyar na yankin Igbo sun kasance cikin zullumi da fargaba biyo bayan umarnin zaman gida da kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biafra ta bayar.

https://p.dw.com/p/3uFCx
NIGERIA Biafra Aba Demonstration
Gangamin masu rajin kafa kasar Biafra a kudancin NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Ranar 31 ga watan Mayu ce rana 'yan kungiyar IPOB suka ayyana a matsayin ranar Biafra wacce suke nufin tuna 'yan mazan jiyan su da suka kwanta dama yayin yakin basasar Najeriya tare da fatan sake shata sabon tsari na ci gaba da fafutikar kafa kasar Biafra da ta hada har da yankin Niger Delta mai arzikin manfetur. DW ta zanta da Mr Kenneth, wani tsohon sojan Biafra game da ranar, yana mai cewa "Muna tunawa da wannan rana ta 'yan mazan jiya da suka kwanta dama a yayin yakin basasa, sannan kuma muna juyayin rajin kafa kasar Biafra, ni din nan ina cikin sojojin da suka yi yaki don kafa Biafra, dan haka a yau da muke zaman gida cike muke da farin ciki."

Karin bayani: Tabarbarewar tsaro a Najeriya

Nigeria pro-Donald-Trump-Kundgebung der Indigenous People of Biafra in Port Harcourt
'Yan rajin kafa Biafra a Port HarcourtHoto: Getty Images/AFP

Wani daga Jahar Ebonyi yankin kudancin Najeriya mai suna Mr Clement Nnaji, ya sheda wa wakilin DW cewa ba a iya ganin kowa kan titiunan birnin, haka kuma hada-hadar yau da kullum ta tsaya ba kamar yadda ake gani a kowace rana ba. "Daukacin mutane sun bi umarnin kungiyar rajin kafa Biafara, an rufe makarantu an rufe kasuwanni an rufe bankuna." Ga dukkanin alamu rashin fitowar jama'a na nuna bin umarnin IPOB, kana kuma a share daya, hakan na nuna dari-darin da jama'a ke da shi na fitowa don kaucewa tashe-tashen hankula, ganin yadda yadda 'yan kungiyar IPOB din suka rika tada hankulan jama'a, ta hanyar kaddamar da hare-hare da suka yi sanadiyar mutuwar al'umma, baya ga kone-kone a sassan yankin a kwanakin baya bayan nan.

Karin bayani: Najeriya: Shekaru 50 da kammala yaki

Demonstration für politischen Aktivisten Nwannekaenyi Nnamdi Kenny Okwu Kanu
Wani dauke da hoton Nnamdi Kenny Okwu KanuHoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

Daman dai jama'a a wannan yankin duk abubuwan da ke faruwa a baya tamkar share fage ne ga abin da ka iya afkuwa wannan rana, duba da yadda suka jima suna ganin dauki ba dadi tsakanin 'yan kungiyar IPOB da jami'an tsaro da ke kara firgitar da jama'a ire-irensu Malam Hamza, wani dan chanji da ke zaune a birnin Owerri na Jihar Imo da aka kashe Alhaji Ahmad Gulak, inda kuma 'yan IPOB suka fi tsananta kai hare-harensu a baya bayan nan. Hamza cewa ya yi "Yanzu haka muna zaune ba inda muka tafi, kuma kowa ya rufe shagonsa ba wanda ya bude."

Karin bayani: IPOB na shirin zaman dirshan a Najeriya

Sai dai an tabbatar da bindige wasu mutane da suka hada da wani babban mai shari'a a daya daga titunan birnin Enugu, haka da wani jami'in gwamnati a Owerri Jihar Imo, da kuma wani dan Okada da yai wautar fita a Awka na Jihar Anambra, kana kuma an ta jin karar harbe-harbe a wasu sassan birnin Owerri.

Bisa la'akkari da karancin tashe-tashen hankula da kashekashen da aka fuskanta a wannan rana, sabanin irin yadda kungiyar IPOB ta saba yi, ya tabbatar da cewa rundunonin tsaro na 'yan sandan Najeriya da soja da na 'yan sandan ciki na DSS sun taka rawar gani, wajen aikin kare rayuka da dukiyoyin jama'a.