Neman hanyar magance tashin farashin abinci
February 7, 2024
Kuma cikin kasa da tsawon wattani guda Biyu da girbe abincin, farashin kayan gona ya nunka tare da tada hankali miliyoyi na yan kasar dake fuskantar yunwa. Shinkafa dai ta kai 70, haka ma farashin masara ya wuci 60, manya na bukatun cikin gidaje na kasar, amma kuma ke neman kamshi irin na dan goma a yanzu. Akwai dai tsoron rikici a bangare na 'yan kasa, bayan alamu na zanga-zangar cikin garin da ta tada hankalin yan mulki na kasar. To sai dai kuma wani taron majalisar samar da tsaro na abincin ta ce tai nisa a kokarin tunkarar matsalar da kila ma kai ta zuwa tarihi a lokaci na kankane.
Karin Bayani: Najeriya: APC ta zargi PDP da hannu a zanga-zangar kasar
Duk da cewar dai sai kusan a gobe ne 'yan mulkin ke shirin sanar da dabarun, majiyoyin zauren taron dai, sun ce Abujar na shirin ta leka rumbu da nufin kwashe daukaci na kaya na abincin da sai dasu tsakanin al'umma a rahusa. To sai dai kuma kalubalen dake gaban yan mulkin dai na zaman rashin isashen abincin da ke a rumbunan kasar a halin yanzu. A gaba daya dai yawan Abincin da ke zaman a mallakin gwamnatin bai wuci tan 56,000 ba ga kasar da kusan kaso 70 cikin dari na yayanta ke da bukata ta agajin a halin yanzu.
Akwai dai tsoron komawa zuwa ga kasuwa da nufin kara wan ina iya kaiwa ga kara tashi na farashi da kila jefa daukacin kasar cikin wani rikicin. Mahukunta na kasar dai sun zura ido tare da kyale masu kasuwar kasar da kila ma na makwabta wasoso cikin hatsin kasar a shekarar bana. Wani sabon shiri na noman rani da kasar ta kaddamar wattani yiyu baya ne dai ke zaman sabon fatan tunkarar matsalar da ke zaman mai girma yanzu haka. Fadar mulki ta Abuja dai na a tsakanin samar da isashe na abinci da nufin rage radadi na yan kasar dake fuskantar tsadar makamashi, da kyale rikicin na abincin kaiwa zuwa babbar barazanar da ka iya shafar daukacin makoma ta kasar.