kalubalen Najeriya bayan shekaru 61 da 'yancin kai
October 1, 2021Najeriya ta dora ga shekaru sittin a cikin halin rudani da ma rashin tabbas na makoma ga kasar dake tsaka a cikin rikicin rashin tsaro da siyasa ta kabilanci. Kuma kama daga sashen arewacin kasar zuwa na kudancinta hadarin rikicin ya jima yana cidar da ta dauki hankalin shi kansa shugaban kasa da ya share lokaci yana neman hada kan yan kasar.
Shugaba Muhammadu Buhari yace yana iyakacin kokari domin shawo kan jerin matsalolin Najeriya, walau na rashin tsaro ko kuma rikici na tattalin arzik. To sai dai kuma yace babu gudu babu jada baya bisa makoma ta hadin kan Najeriyar wuri guda komai rukuki yana mai cewa " Najeriya tamu ce gaba daya kuma babu wani abun da zai iya jawo matsala ga hadin kanta. Nasararta za ta tabbata ne in har muka hadu wuri guda da tunanin samun zaman lafiya da ci gaban al'ummarmu.
Karin Bayani: Najeriya: Shekaru 60 da samun 'yanci
Zamu cigaba da neman hanyoyin warware banbance-banbancenmu cikin masalaha. Amma kuma a shirye muke domin daukar tsatsauran mataki ga masu neman da ta ware da masu daukar nauyinsu. Kamen Nnamdi Kanu da Sunday Adeyemo sun fitar da sunayen wasu manyan masu daukar nauyinsu. Kuma mun fara bin wadanda suke daukar nauyin da suka hada da wani dan majalisar tarraya." Sannu a hankali dai Shugaba Buhari na dada nisa a cikin jagorancin kasar da hankalin yayanta ke rabe bisa addini da kabila dama makoma ta shugabanci a gaba. Jerin rigingimun na tada hankali na da dama cikin kasar dake ganin da sauran gyara.
Karin Bayani: Najeriya: Makomar masana'antar man fetur
Mohammed Sale Hassan shugaban kungiyar "One Nigeria” mai neman hada kan yan kasa ya bayana cewa "Akwai abun koyi daga tarihin rikicin kabilancin da ya faru a kasar Rwanda, saboda haka sai an yi taka tsan-tsan." Abun jira a gani na zaman iya kaiwa ga gaci a fagen siyasar ba tare da yin illa ga tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Najeriya ba.