Amfani da hanyar sadarwa a zaben Najeriya
October 13, 2021Matakin majalisar dai, ya biyo bayan matsin lamba daga 'yan adawa musamman na jamiyyar PDP da masu fafutuka da ke ganin zai taimaka wajen samar da sahihin zabe a kasar. Wannan batu dai ya dade yana jawo kace-nace, a aikin gyaran fuskar da ake yi wa dokokin zaben Najeriyar. Da ma dai majalisar tarayya ce ta fara amincewa da matakin, abin da ya sanya dole aka samu daidaito a kan dokar.
Ta dai kai ga hukumar ta INEC sanya baki, inda ta ce ita dai tana da kayan aikin da za ta iya tattaro sakamakon zabe ta amfani da Internet din. A daya bangaren kuma majalisar dattawan ta amince da a yi amfani da tsarin 'yar tinke a zaben fitar da gwani na jamiyyu, domin kawar da amfani da wakilai ko delegate. Kungiyoyin farar hula da ke rajin kyautata zabe a Najeriya da suka sanya baki wajen matsin lamba ga majalisar, na cike da fatan wannan zai taimaka wajen samar da sahihin zabe a kasar.