Rikici tsakanin 'yan bindigar Niger Delta
October 18, 2023Tsoffin kungiyoyin dai na adawa da bawa mutum daya tilo kwangilar tsaron bututun mai a yankin inda suka bukaci sake fasalta kwangiyar domin kowa ya samu.
Wannan rigima dai da wasu tsoffin shugabannin kungiyoyin 'yan bindigar yankin na Niger Delta suka bujiro da ita a yanzu, kan kwangilar tsaron bututayen danyen mai ta kimanin Naira biliyan 58, wanda tsoffin 'yan bindigar irin su Mujaheed Asari Dokubo na kungiyar Niger Delta Volunteer Force, da Tom Ateke na Niger Delta Vigilante suka yi kira a sake fasali.
Mack Martins, mai magana da yawun Asari Dokubo ya bayani yana mai cewa:-
"Yace magana ce kawai ta nuna adalci, domin ware mutum daya a bashi wannan kwangila ba daidai ba ne, kuma ina ganin kamar gwamnati ta ji wannan korafi, a bawa kowane bangare na tsoffin 'yan bindigar nasa kason".
Karin Bayani: Tsagerun Niger Delta na barazanar komawa ruwa
Tsoffin shugabannin 'yan bundugar na korafi ne kan kwangilar biliyan 58 da a hukumance aka bai wa kamfanin TANTITA, mallakar tsohon dan bindiga na kungiyar MEND a yankin. Kuma dama tun gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari aka ba wa TANTITA wannan katafariyar kwangila da hakan ya jawo cece-kuce tun a lokacin, sai dai batun sabunta wa'adin kwangilar ga kamfanin na TANTITA, shi ne ya zamo babban batu na rikici da kuma adawa mai zafi a yanzubwanda ga alamu idan gwamnatin Najeriya ba ta yi hattara ba, yankin na Niger Delta na iya komawa sabon rikici, rikici da zai iya shafar ayyukan hako danyen mai a yanki.
Mr Asiaye Enaibo, shi ne mai magana da yawun Government Tompolo mai kamfanin TANTITA da aka bai wa kwangilar ta tsaron bututayen man.
"Ya ce a bayyane ta ke an yi fafutuka a wannan yankin, kuma Tompolo na a kan gaba wajen wannan fafutuka ta 'yantar da yankin na Niger Delta,kuma Tompolo dan dara sa'a ne, don haka da wannan kwangila ta fito an yi ta cece-kuce, musamman su Asari Doku, da Tom Ateke da sauran su, cewar wannan kwangila sai dai a kacaccala ko wane bangare ya samu, basu san hanyoyin da muka bi a hukumance muka samu wannan kwangila ba,wannan ita ce rigimar da a ke ciki".
Yanzu dai, wasu alkaluma na nuni da cewar, kamfanin man NNPCL ya sabunta kwangilar ga kamfanin TANTITA, wanda tsoffin 'yan bindiga da dama ke ci gaba da nuna adawa shi.
Rikicin 'yan bindigar Niger Delta dai ya fara tsananta ne a shekarar 2004, inda kungiyoyi da dama suka rika fasa bututayen mai, tare da garkuwa da ma'aikatan mai bisa hujjar cewar ba a yi wa yankin adalci a arzikin man da Allah ya huwace mata. Shirin afuwa na tsohon shugaba Ummaru Musa Yaraduwa, shi ne ya fara kwantar da kurar rikicin yankin.