Senegal: Matsin lamba kan jadawalin zabe
February 22, 2024Wanna na zuwa ne a daidai lokacin da wata sanarwar da ta fido daga fadar shugaba Macky Sall mai barin gado da ta ce zai yi jawabi wa al'ummar kasar a maraican ranar Alhamis 22.02.2024. Gamayyar jam'iyyun da ke mara baya wa dan takara Diomaye Faye ta zargi shugaba Sall da jan kafa da kuma yin wasa da hankalin 'yan siyasan kasar wajen shirya zabe.
Gamayyar jam'iyyun adawan ta kuma bukaci hukumomin Dakar da su gaggauta sallamar dukannin fursunonin siyasa da aka tsare a gidajen yari kan rikicin siyasan kasar daga shekarar 2021 i zuwa wannan lokaci.
Shi dai Bassirou Diomaya Fayeda ke zama daya daga cikin gwamman 'yan takara da aka tantance na tsare a gidan kaso tun a watan Afrilun 2023 ba tare da ya fuskanci shari'a ba.
Kazalika gamayyar ta jaddada cewa tana kan bakanta na a gudanar da zabe kafin karshen wa'adin mulkin Macky Sall wanda ke karewa a ranar biyu ga watan Afrilu mai zuwa.