Takaddama a Najeriya a kan Shaidar digiri daga Togo da Benin
January 3, 2024Wani binciken sirri na wata kafar labarai da ke zaman kanta a tarrayar Najeriya ne ya tayar da tsohon miki bisa takardun shaidun kammala digiri da ke fitowa daga makwabtan kasashen guda biyu wato Togo da Benin. A cikin mako shida ne wani dan jarida ya kammala digiri ba tare da leka birnin Cotonou domin daukar darasin da ke iya ba shi damar samun shaidar ba.
Karin bayani:Makomar ilimi a kasashe masu fama da rikici
Wannan bincike ya tayar da hankalin 'yan mulkin tarrayar Najeriya, tare da kai ga dakatar da amincewa da takardun shaidar digiri daga kasashen na Togo da Jamhuriyar Benin. Hukumar kula da jami'o'i ta kasar ta kuma dakatar da wasu jerin jami'o'i guda 18 da ke zaman na kasashe na waje, amma ke ba da takardun shaida daga tarrayar Najeriyar.
Karin bayani:Najeriya: Mecece makomar karatun jami'a?
Daruruwan daliban Najeriya ne ke tsallakawa zuwa ga makwabta don neman sauki, ko kuma kokarin kauce wa rikici a yunkurin neman shaidar da ke da tasiri ga rayuwa da makomar al'umma ta kasar. Wata sanarwa ta kungiyar dalibai ta tarrayar Najeriya ta ce kuskure ne da ke da girman gaske na gaza bambance tsakanin karatun da ke zaman na hakika da kuma na bogi cikin karatun kasashen guda biyu.
Karin bayani:Halin da ilimi ke ciki a Najeriya da Nijar
Daga dukkan alamu dai, barnar na shirin yin tasiri cikin Najeriya, inda dalibai da daman gaske ba su iya ko da rubuta wasikar neman daukar aiki a kamfanoni na kasar ba. Farfesa Abdulkadir Mohammed da ke zaman jigo na kungiyar malaman jami'o'i na kasar ASUU, ya ce in daddawa tana da warin gaske, to shi ma bera ya yi nisa a sana‘ar sata.
Karin bayani:Karin kudin karatu a jami'o'in Najeriya
Batun yajin aiki a jami'o'i na kasar da kila ma kasawa na zaman na kan gaba a tururuwa ta neman ilimin mai sauki. Umaru Audu da ke zaman dan jaridar da ya yi shigar burtu ya kuma yi nasarar samun digiri a makonni Shida ya ce rudun na da girman gaske a cikin batun ilimin.