Likitoci na yajin aiki duk da karuwar cututtuka
August 3, 2021Al’ummar da suka je neman lafiya a yawancin asibitocin Najeriya sun shaida rashin ganin likitoci da ke duba su inda wasu kuma da ke kwance a asibitoci ba a sallame su ba don sun warke, saboda yajin aikin da likitoci da ke neman kwarewa su ka shiga. Shugabannin kungiyar likitoci masu neman kwarewa wanda su ka karci kasa da nuna cewa rashin cika musu alkawari da gwamnatin najeriya ta yi ne ya sa fadawa wannan yajin amma ba da son ran su ba.
Daga cikin likitoci dubu 40 da ake da su a fadin kasar kimanin dubu 16 ne su ka fantsama yajin aikin wanda tuni ya fara tasiri tare da shafar masu neman lafiya musamman a asibitocin gwamnati. To sai dai tuni al’umma da masu ruwa da tsaki a harkokin lafiya da sauran masana su ka fara nuna damuwa kan halin da za shiga ganin Najeriya na fuskantar barazanar cutar COVID-19 kashi na uku wanda ake kira Delta da kuma yadda ake fama da yaduwar cutar kwalara da yanzu haka ta bulla a jihohin 18 da Abuja.
Karin Bayani: Kalubalen annobar Corona a Najeriya
Dr Yarma Ahmad Adamu shi ne shugaban aisbitin Yarma a Najeriya ya ce "Ya zama dole gwamnati ta gaggauata sansantawa da wannan likitoci cikin ‘yan kwanaki masu zuwa saboda muhimmancin su." Masu gwagwarmayar taimakawa al’umma cewa su ka yi idan "beera da sata to daddawa ma na da wari" kamar yadda Ibrahim Garba Wala shugabar gidauniyar "GivFree Africa" ya shaida wa DW, inda ya ce " Likitocin da ke yajin aiki a asibitocin gwamnati ko masu zaman kansu, kamata ya yi su hada hannu da gwamnati su fahinci juna don ceton rayukan al'umma."
Karin Bayani: Makomar fannin kiwon lafiya a Najeriya
Likitocin da ke yajin aiki sun ce sun jima su na daga kafa wa gwamnati amma ta yi kunnen kashi kan bukatunsu. Dr Abubakar Kaka Sanda shi ne shugaban Kungiyar likitoci masu neman kwarewa da ke Asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri cewa yayi. Akwai wasu ma'aikatan da suka shafe tsawon watanni fiye da 10, saboda hakan an jima ana tattauna wa kafin wannan yajin aikin." To amma a cewar Dr Kole Shetima shugaban cibiyar wanzar vda Demokradiyya ya zama dole a samo mafita ta dindindin kan wannan matsala. Yanzu haka wannan yajin aikin ya sa kasuwar asibitoci masu zaman kansu ta bude inda masu karfi ke garzayawa don samun kulawar lafiya inda mutane ‘yan Rabbana ka wadata mu ke zuwa wajen masu magungunan gargajiya don samun taimako.