1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLibiya

Al'ummar Derna sun yi zanga-zanga

September 18, 2023

Al'ummar birnin Derna sun gudanar da zanga-zanga domin bukatar gwamnatin da ke ikon Gabashin Libiya da ta ba da bahasi kan munmunar ambaliyar ruwa da birnin ya fuskanta.

https://p.dw.com/p/4WUQo
Mazauna Derna I Libiya I Zanga-zangar adawa da matakan gwamnati
Mazauna Derna I Libiya I Zanga-zangar adawa da matakan gwamnatiHoto: Zohra Bensemra/REUTERS

Masu aiko da rahotanni sun ce darurruwan mazauna birnin Derna sun yi cincirundo a gaban wani babban masallaci suna rera kalaman batanci da kuma adawa da mahukuntan Gabashin kasar da kuma majalisar yankin.

Karin bayani: Guguwa da ambaliya sun kashe rayuka a Libiya

A cikin sanarwar da masu zanga-zangar suka karanta sun yi kira da a gaggauta gudanar da bincike da kuma gufarnar da wadanda ke da alhakin balakin da yankin ya fuskanta a gaban shari'a. Sannan kuma sun yi kira da a gaggauta buda wata cibiya ta MDD wacce za ta samar da tsarin sake gina birnin na Derna da kuma biyan diyya ga wadanda lamarin ya shafa.

A daya gefe kuma masu zanga-zangar sun bukaci da a rusa majalisar da ke tafiyar da birnin tare da gudanar da bincike kan kasafin kudin birnin na shekarun baya.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da aike tallafi wa Libiya, na baya-bayan nan shine tallafin miliyan 5,2 na yuro da Tarayyar Turai ta alkawalta ba wa kasar.

Karin bayani: MDD: Libiya na bukatar taimako