Amurka ta fanshi fursunoninta da Iran ta tsare
September 18, 2023Kimanin dala biliyan shida ne Amurka ta bura wa Iran ta hanyar bankunan Qatar, a wani mataki na share fagen musayar fursunoni da kasashen biyu za su yi.
Karin bayani: Takaddama kan kudaden Iran da Amurka ta rike
Majiyoyi da dama sun ce tuni wani jirgin saman Qatar ya isa Teheran babban birnin Iran, da nufin jigilar fursunonin biyar dukanninsu Amurkawa da kuma wasu 'yan uwansu guda biyu. Daga cikin fursunonin har da hamshakin mai kudin nan Siamak Namazi, wanda hukumomin Iran suka tsere tun a shekarar 2015 bayan da kotun ta yanke masa hukuncin dauri na shekaru 10 bisa zarginsa da aikata laifin leken asiri.
Karin bayani:Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mutum uku
Wannan musayar fusnoni na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Iran Ebrahim Raissi ke shirin isa birnin New York na Amurka inda zai halarci taron koli na Majalisar Dinkin Duniya.