1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daruruwan fursunoni sun tsere a Najeriya

Uwais Abubakar Idris AMA(SB)
July 6, 2022

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar gani da ido a gidan yarin Kuje da ke Abuja, inda ‘yan bindiga suka kai hari da bama- bamai tare da sakin sama da fursunoni 800

https://p.dw.com/p/4DlyB
Nigeria | Hari kan gidan yarin Kuje da ke Abuja
Nigeria | Hari kan gidan yarin Kuje da ke Abuja Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Mumunan hari da 'yan bindiga suka kai ya rusa kofar shiga gidan yarin, tare da kona motoci da dama da suka iske. Harsasai sun illata ginin gidan yarin a harbe-harbe da bata kashi da jami'an tsaro suka yi da maharan.

 Shugaban Najeriya ya isa wurin tare da sauran manyana jami’an tsaron najeriya, inda ya zagaya ya da duba abinda ya faru. A bayyane take cewa ransa ya baci, kuma ya girgiza da harin da aka kai a gidan yarin.

Daruruwan fursunoni sun tsere bayan hari

Bayanai sun tabbatara da cewa sama da fursunoni 800 ne suka tsere a lokacin da aka kai wannan hari, amma jami’an gwamnatin sun ce 600 daga cikin fursunoni kusan dubu guda da ke gidan yarin suka balle. Akwai gwamman jiga-jigan kungiyar Boko Haram da hukumomi ke cewa suna tsare a cikin gidan, baya ga fursunonin siyasa. 

Karin Bayani: Tsofaffin sojoji a yaki da ta'addanci a Najeriya

Nigeria | Hari kan gidan yarin Kuje da ke Abuja
Nigeria | Hari kan gidan yarin Kuje da ke Abuja Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Maharan sun saki kusan daukacin fursunonin, in banda wadanda ake tsare da su bisa dalilai na siyasa. Sai dai babban sakatare a ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar, Shuaib Belgore, ya shaida cewa sun yi nasarar kamo fursunoni 300 daga cikin 600 da suka tsere. 

Ana diga ayar tambaya bayan harin Kuje

Hari irin wannan a wurin da ke da cikakken cikakken tsaro na 'yan sanda da sojoji ya jefa tambayoyi maban-banta a zukatan jama'a a kan shin me ya faru ne kuma ya aka yi aka kai wannan bari bayan gwamnati ta dade tana alwashin ba za ta sake bari a kai irin wannan hari ba? Anya babu sakaci a cikin lamarin?

Karin Bayani:  Dubban makamai sun bace a Najeriya 

A baya 'yan bindigan sun kai irin wadannan hare-hare a gidajen yarin Najeriyar da dama, ta hanyar amfani da bama-bamai da harbi na kan mai uwa da wabi da suka kai 300, amma ba’a kama koda mutum guda ba ya zuwa yanzu ba, abin ya zaman na damuwa da nuna hali na yanayin tsaro a Najeriyar.