Tinubu ya mika kasafin kudinsa na farko
November 29, 2023Kasafin kudin da ya kama Naira tiriliyan 27 da biliyan 500 dai, ya tanadi Naira tiriliyan takwas da biliyan 700 domin manyan ayyuka a yayin da Naira tiriliyan tara da biliyan 92 za su tafi ga ayyukan yau da gobe. A shekarar da ke shirin kama wa dai, kasar za ta biya bashin da ya kai Naira tiriliyan takwas da biliyan 25. An dai gina kasafin kudin ne a kan gibin da ya kai Naira tiriliyan tara da biliyan 18, gibin kuma da gwamnatin take fatan ta cike shi daga wani sabon bashin da kasar za ta ciwo na kimanin Naira triliyan bakwai da biliyan 83.
Karin Bayani: An yi karin kasafin kudin Najeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriyar dai ya ce kasafin na "sake dora sabon fata" zai dogara ne kan gangar mai miliyan daya da dubu 78 da gwamnatin take fatan ta haka kullum, tare da sai da kowace ganga kan dalar Amurka 77. Batun tsaro da ayyukan yi ne dai ko bayan rage fatara, a fada ta shugaban zai dauki hankalin mahukuntan a shekarar da ke kamawa. Kasafin dai na da burin samar da ci-gaban tattalin arzikin da zai samar da ayyukan yi a tsakanin al'umma. Haka kuma zai kai ya zuwa daidaito a harkar kudi, da kuma ingantaccen yanayin zuba jari. Ko bayan nan dai akwai kuma fatan habaka damarmakin al'umma da kuma rage fatara da samar da rayuwa mai kyau.
A cewar Shugaba Tinubun sun kuma bayar da fifiko kan batun tsaro da zaman lafiyar al'umma, haka kuma akawai shirin gyaran fuska ga tsarin tsaron domin inganta damar jami'an tsaro ta bayar da kariya ga dukiya da rayuka a ko'ina cikin kasar. Duk da cewar dai sai a nan gaba ministan kudin Najeriyar yake shirin bayyana dalla-dallar kasafin zuwa ma'aikatu da hukumomi na gwamnati, tuni dai jawabin shugaban kasar ya dauki hankalin 'yan dokar da ke shirin kallon tsaf a kansa. Sanata Abdurahamman Kawu Sumaila na wakiltar jihar Kano a zauren majalisar dattawa, kuma ya ce suna zaman jiran karatun karen gidan biki.
Karin Bayani: Dakile fasa kwabrin makamai a Najeriya
In har masu adawar suna zaman jira su kansu masu tsintsiyar da ke a zauren dokar sun ce da kamar wuya yabon dan kuturu, a fadar Aminu Sani Jaji da ke zaman dan majalisa da ga jihar Zamfara. An dai dade ana ruwa kasa na shanyewa a kokarin tunkarar annobar ta tsaro, annobar kuma da ke zaman ta kan gaba wajen yin tarnaki a Tarayyar Najeriyar. Aminu Balele dai na zaman dan majalisar wakilai ta kasar daga Katsina, kuma ya ce akwai alamun Tinubun ya dauko hanyar tunkarar nnobar da ke ta tashi da lafawa tun tsawon lokaci. Sabon kasafin dai, na zaman zakaran gwajin dafi tsakanin Tinubun da miliyoyin 'yan kasar da ke zaman jiran cikon alkawari na siyasa a cikin halin kunci.