You need to enable JavaScript to run this app.
Tsallake zuwa shafin jadawali
Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bidiyo
Shirye-shiryen DW Hausa
Yankuna
Najeriya
Nijar
Afirka ta Yamma
Sassa
Siyasa
Zamantakewa
Wasanni
Mayar da hankali
Ilimin Fasahar Zamani
Shirye-shiryen DW Hausa
Bidiyo
Talabijin kai tsaye
Talla
Guguwar Neman Sauyi
Guguwar neman sauyi ta kada a kasashe da dama na Larabawa inda mutane suka bukaci sauyin shugabanci.
Tsallake zuwa bangare na gaba Duk abin da ya shafi wannan maudu'i
Duk abin da ya shafi wannan maudu'i
Binciken take hakkin dan Adam a Gaza
Majalisar Dinkin Duniya ta kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan batun take hakkin dan Adam da ake zargin Isra'ila ta aikata a yankin Zirin Gaza.
Kotun Masar ta haramta jam'iyyar FJP
Reshen siyasa na kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka fi sani da FJP ba zai iya tsayar da 'yan takara a zabukan Masar ba saboda kotu ta sokeshi daga fagen siyasa.
Tsugune ba ta kare ba a Zirin Gaza
Tattaunawar da aka yi tsakanin Falasdinawa da Isra'ila a kasar Masar ta watse ba tare da cimma wata matsaya ba.
Isra'ila ta ce ba za ta halarci taron Masar ba
Isra'ila ta ce ba za ta shiga tattaunawar neman sulhu ba da Masar ta shirya domin samun masalha tsakaninsu da Hamas, saboda garkuwa da Hamas ke yi da wani sojinta.
An kai sabbin hare-hare a ƙasar Masar
Hukumomin tsaro sun ce wasu mutane ɗauke da makamai sun kai hari a kan wani wurin binciken da ke kan iyaka da Libiya.
Shugabannin Isra'ila na nazarin sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta
Wakilan Isra'ila da ke halartar wani taro a Masar sun amince da shirin tsagaita wuta na dindindin don kawo karshen rikicin Gaza.
Boren tunawa da hambarar da Morsi a Masar
'Yan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi na niyar tayar da kayar baya sakamakon cika shekara guda da hambarar da shugabansu Mohamed Morsi daga kujerar mulki.
Shekara guda bayan kawar da mulkin Mursi a Masar
Shekara guda da kawo ƙarshen mulkin zaɓaɓɓen shugaban Masar Mohammed Mursi, akwai alamun cewar jam'iyyarsa ta yan uwa musulmi tana farfaɗowa.
John Kerry na ziyara a kasar Masar
Sakataran harkokin wajan Amirka John Kerry ya gana da Abdel Fattah Al-Sissi, na Masar kan rikicin Iraki inda ya ce rikicin babban barazana ne ga Yankin Gabas Ta Tsakiya
Ƙoƙarin murƙushe 'yan adawa a Masar
Kotu a Masar ta tabbatar da hukuncin kisa a kan shugaban Ƙungiyar 'yan Uwa Musulmi da kuma wasu magoya bayan ƙungiyar 182.
An rantsar da Firaministan kasar Masar
Shugaban gwamnatin kasar Masar Ibrahim Mehleb, tare da ministocinsa, sunyi rantsuwar kama aiki a wani mataki na fuskantar kalubanen dake gabansu.
Za a saki dan jaridar da aka kama a Masar
Rahotanni daga Masar na cewar an bada umarnin sakin dan jaridar na Al-Jazeera da ke yajin cin abinci bayan da aka tsare shi ba tare da yi masa shari'a ba.
Al-Sisi ya zama shugaban Masar na takwas
An rantsar da tsohon hafsan soji Abdel Fattah al-Sisi a matsayin sabon shugaban Masar a harabar kotun tsarin mulkin kasar, tare da tsaurara matakan tsaro.
Marshal Al Sisi ya lashe zaben shugaban kasa a Masar
Bayan da hukumar zaben Masar ta bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da tace, Fil Mashal Al Sisi ne ya lashe da gagarumin rinjaye, yan kasar da ma kasashen Larabawa na ci gaba da yin martini kan zaben.
Marshal Al-Sisi ya lashe zaben shugaban kasa a Masar
Bayan da hukumar zaben Masar ta bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da tace, Fil Mashal Al Sisi ne ya lashe da gagarumin rinjaye, yan kasar da ma kasashen Larabawa na ci gaba da yin martini kan zaben.
Abdel Fattah al-Sissi ya samu nasara a zaɓen Masar
Sakamakon farko na zaɓen da hukumar zaɓen ƙasar Masar ta Bayyana na nuna cewar Al Sissi shi ne ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka kammala wanda kafofin watsa labarai na ƙasar suka yaɗa batun
Abdel Fattah al-Sissi ya samu nasara a zaɓen Masar
Sakamakon farko na zaɓen da hukumar zaɓen ƙasar Masar ta Bayyana na nuna cewar Al Sissi shi ne ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka kammala wanda kafofin watsa labarai na ƙasar suka yaɗa batun.
An fara kada kuri'u a zaben shugaban kasar Masar
Tsawon yini biyu ne dai, Misirawa za su kwashe a zaben shugaban kasar da ke gudana, wanda tuni ake ganin dan takara Al-Sissi ne zai yi nasara.
Yaƙin neman zabe na Masar ya kankama
Yayin da ake shirin zaɓen shugaban ƙasar Masar cikin wannan wata na Mayu, ɗaya daga cikin abubuwan da suka fito fili shi ne cewa Abdul-Fattah al-Sisi zai lashe zaɓen.
Dan Masar ya lashe lambar yabo ta Bobs 2014
Marubucin blogs mai kuma daukar hoto ga jaridu dan shekaru 23 daga kasar Masar ya lashe babbar lambar yabo ta Bobs ga masu fafatuka ta intanet.
An fara yakin neman zabe a kasar Masar
Janar Abdel Fatah al-Siisi da ke da goyon bayan sojoji da kuma Hamdine Sabbahi da 'yan adawa suka tsayar ne za su fafata a zaben shugaban kasa a Masar.
Kara kuntatawa 'yan adawa a Masar
Mahukuntan Masar sun kara zafafa matakan da suke dauka a kan kungiyoyi da sauran wadanda ke adawa da mulkinsu, inda suke amfani da alkalan kasar.
An kai hare-hare a ƙasar Masar
Hukumomin tsaro a sun ce wani janar na 'yan sanda ya rasa ransa a sakamakon fashewar wasu abubuwan guda biyu a birnin Alƙahira.
An kashe masu zanga-zanga a Masar
Mutane aƙalla guda biyar aka kashe a birnin Alƙahira a lokacin wani yamutsin da magoya bayan Ƙungiyar 'Yan Uwa Musulmi suka gudanar.
Amirka ta yi tir da hukuncin kisa a Masar
Kwana guda bayan da kotu ta yanke wa wasu mutane sama da 500 hukuncin kisa a Masar, wasu 'yan adawa 700 da su ma za su iya fuskantar hukuncin kisan sun gurfana a gaban kuliya.
An gurfanar da wasu ƙarin 'yan adawa a Masar
Daga cikin waɗanda aka gurfanar har'da Mohammed Badie jagoran Ƙungiyar 'Yan Uwa Musulmi.
Amirka ta nuna damuwa ga hukuncin kisa a Masar
A wannan Litinin dai wata kotu a kudancin Masar ta yanke hukuncin kisa ga wasu daruruwan mutane da akasarinsu magoya bayan kungiyar 'Yan uwa Musulmi ne.
Gwamnatin kasar Masar ta yi murabus
Gwamnatin da sojoji suka girka a kasar Masar ta mika takardar murabus dinta ga shugaban rikon kwaryar Adly Mansour.
Badakalar siyasar kasar Masar
Shugaban rundunar sojojin kasar Masar da ya jagoranci kifar da zababbiyar gwamnatin Dimokaradiyar kasar, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.
Martanin Misrawa kan takarar al-Sisi
Al'ummar Masar na ci gaba da nuna goyon bayansu ga takarar Abdulfattah al-Sisi wanda bayan an yi mi shi ƙarin girma, ana sa ran zai ajiye aikin soji ya shiga siyasa.
Martanin 'yan Masar kan takarar Al-Sisi
Al'ummar Masar na ci gaba da nuna goyon bayansu ga takarar Abdulfatah al-Sisi wanda bayan an yi mi shi ƙarin girma, ana sa ran zai ajiye aikin soji ya shiga siyasa
Sosoji a Masar sun amince da takarar Al-Sissi
Sojojin kasar Masar sun bada amincewarsu ga takarar Janar Abdel Fattah al-Sissi, a matsayin dan takara a zaben shugaban kasar da za a yi nan gaba a kasar.
Mutane kusan 30 sun hallaka a kasar Masar
Rikicin da ya barke a kasar Masar tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga ya yi sanadiyar mutuwar mutane masu yawa
Jirgin sama mai saukar ungula na sojojin Masar ya fadi
Wannan ya hadari ya afku ne yayin da ake tunawa da shekaru uku da fara boren da ya kawo karshen gwamnatin Hosni Mubarak ta kasar Masar
Ruwan bama-bamai a kasar Masar
Mutane shida sun hallaka a kasar Masar bayan da wasu bama-bamai hudu sukia tashi a Alkahira babban birnin kasar.
Tashin bama-bamai sun ruɗa birnin Alƙahira
A kasar Masar an samu fashewar wasu ababai da ake kyautata zaton bam ne a gaban hedkwatar rundunar 'yan sandan da kuma a tashar jiragen ƙasa a babban birnin ƙasar.
Rigingimu da cin zarafin 'yan adawa sun karu a Masar inji Amnesty
Kungiyar Amnesty International ta bayyana cewa Masar ta shiga wani yanayi na tashe-tashen hankula maras misali, tun bayan da sojojin kasar suka kifar da gwamnatin Mohamed Morsi.
Ƙuri'ar raba gardama na gudana a Masar
Mutune 5 sun rasu, yayin da jami'an tsaron Masar suka fasa wani gangamin masu adawa da juyin mulkin soji, lokacin da 'yan ƙasar ke kaɗa ƙuri'ar raba gardama bisa kundin tsarin mulki
Zanga-zanga a Masar kan Mursi
An dage sauraron karar tsohon Shugaban Masar Mohamed Mursi
Rikicin Masar na daukan sabon salo
Dalibi daya ya rasa ransa cikin artabu tsakanin jami'an tsaron kasar Masar da masu zanga-zangar.
Rikicin Masar ya zafafa
Mutane uku sun hallaka yayin dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaron Masar da masu zanga-zanga.
Hukumomin Masar sun tsare mutane da yawa karkashin dokar yaki da ta'addanci
Tun bayan harin kunar bakin wake da aka kai kan wata shelkwatar 'yan sanda da ke birnin Mansura, mahukuntan birnin Alkahira ke matsa lamba kan masu kishin Islama.
Mutane da yawa sun rasu a wani harin bam a shelkwatar 'yan sanda a Masar
Hukumomin kasar sun kuduri aniyar zakulo wadanda ke da hannu a harin don gurfanar da su gaban kuliya.
Tsugune ta ki karewa a Masar
Wani harin Bom da aka kai a kasar Masar ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 14 tare kuma da jikkata wasu da dama.
Shari'ar masu adawa da Mubarak a Masar
Kotun Masar ta yanke hukuncin dauri a gidan maza a kan wasu da suka shiga zanga zangar da ta yi sanadin hambarar da gwamnatin Hosni Mubarak a shekara ta 2011.
Belin masu zanga-zanga a Masar
An bada belin wasu matasa da aka yankewa hukuncin kwanaki 15 a gidan kaso, bayan da suka gudanar da zanga-zanga a Masar.
Saɓani kan sabon tsarin mulki na Masar
Akwai sauran aiki kan rubuta sabon kundin tsarin mulkin ƙasar wanda ake ta yin tankiya akai
Keta dokar tsarin zanga-zanga a Masar
Magoya bayan Kungiyar 'yan Uwa Musulmi sun gudanar da jerin gwano a garuruwan Masar da dama da nufin yin buris da dokar neman izini kafin gudanar da zanga-zanga.
Nuna rashin amincewa da sabuwar dokar Masar
Shugaban Masar ya amince da dokar da ta takaita taron mutane a cikin kasar.
Masar ta kori jakadan Turkiyya da ke kasar
Kasar Masar ta bada sanarwar korar jakadan Turkiyya da ke kasar Huseyin Avni Botsali bayan da ta ce fira ministan Turkiyya ya yi kalamai marasa dadi ga gwamnatin Masar.
Shafin da ya wuce
Shafi 11 daga 18
Shafi na gaba